Saturday, 16 February 2019

PDP ta yi watsi da dage zabe: Tace APC ce ta hada baki da INEC saboda Buhari ya ci gaba da zama akan mulki

Jam'iyyar PDP ta yi watsi da dage zaben da hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta yi inda ta bukaci shugaban hukumar, farfesa Mahmood Yakubu da yayi gaggawar sauka daga mukaminshi domin wannan abu da yayi ya nuna cewa be iya aikiba.A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban jam'iyyar ta PDP, Uche Secondus ya bayyana cewa, dage zaben hadin kaine aka yi tsakanin INEC da jam'iyyar APC bayan da dabarar yin magudi ta karewa APC din. Ya kara da cewa wannan dabarace ta gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari na shirin makalewa a akan kujerar mulki ko ta halin kaka.

Seconduns yace INEC ta yi kone konen kayan aikin zabene da suka wakana 'yan kwanakinnan dan ta yi amfani dashi wajan dage zaben sannan yace itama jam'iyyar APC ta shirya yin amfani da jami'an tsaro wajan tsorata jama'a dan kada su fito zabe.

Ya kara da cewa mutanen da aka kashe a Kaduna yana daga cikin tsarin gwamnan Kadunan da APC dan ganin an tsorata jama'ar yankin kudancin Kaduna ta yanda ba zasu iya fitowa zabe ba tunda APC ta san cewa ba zata samu kuri'u daga yankin ba.

Uche  yace wannan kisa na daya daga cikin shirin gwamnan Kaduna idan aka tuna da maganar da yayi ta cewa za'a mayar da gawarwakin masu sa ido da suka zo Najeriya daga kasashen waje kasashen su inda yace gwamnan yayi hakane dan ya tsorata masu sa idon dan su kauracewa jihar ta Kaduna shi kuma ya samu yayi yanda yake so a lokacin zabe.

Haka itama APC ya yi watsi da dage zaben.

No comments:

Post a Comment