Wednesday, 13 February 2019

Roma ta doke FC Porto

AS Roma ta samu nasara kan FC Porto da kwallaye 2-1 a fafatwarsu ta gasar cin kofin zakarun Turai zagayen farko.Nicolo Zaniolo ya ci wa Roma duka kwallayen biyu, yayinda Adrian Lopez ya ramawa FC Porto kwallo guda.

Rashin nasarar FC Porto ita ce ta farko cikin jimillar wasanni 27 da ta buga a kakar wasa ta bana, ciki harda wasannin gasar zakarun turai na matakin rukuni da bata yi rashin nasara ba, har zuwa matakin yanzu, inda Roma ta samu nasara akanta.

Ranar 6 ga watan Maris kungiyoyin na Roma da Porto za su fafata zagaye na biyu.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment