Sunday, 17 February 2019

Ronaldo ya kafa tarihin shekaru 61 a Juve

Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin shekaru 61 a Juven bayan wasan da suka buga da Frosinone ranar juma'ar da ta gaba wanda aka tashi suna cin 3-0.Ronaldo ne ya ciwa Juve kwallo ta 3 a wasan wadda hakan ta kai yawan kwallaye 19 da yaci a wasanni 24 da ya bugawa Juven, shekaru 61 kenan ba'a taba samun wanda ya taba kafa irin wannan tarihi ba tun tsohon dan wasan Juven John Charles da ya taba yin irin wannan bajinta a kakar wasa ta 1957/58.

Ronaldo ya zama na biyu kenan da ya taba kafa irin wannan tarihi a kungiyar.

No comments:

Post a Comment