Sunday, 10 February 2019

Rwanda za ta fara kera wayoyin Salula

Kasar Rwanda wacce kazamin yakin basasar kabilun Hutu da Tutsi ta durkusar ta yi wa sauran kasashen nahiyar Afirka renon Faransa fintinkau tun a lokacin da ta datse alakar da ke tsakanin ta da Turawan mulkin mallaka.


Bayan muhimman cigaban da ta samu a fannoni da dama,a wannan karon Rwanda ta dauki matakin kafa kamfanin samar da wayoyin tafi da hannunka na zamani wato Smartphone.

Ministan samar da sabbin dabaru,fasaha da kimiyya da kuma sadarwa ta kasar,Paula Ingabire ta ce, suna ci gaba da gudanar musayar da yawu da kamfanonin masu zaman kansu don kafa kamfani na farko wanda zai samar da wayoyin salula.

A cewar labaran kafafan Rwanda,Ingabire ta ce shugabannin kasarta su yanke wannan shawarar da zummar bai wa al'umarsu damar sayen wayoyin tafi da hannun a farashi mai rahusa.

Ingabire ta ce zasu kaddamar da kamfanin a watan Afrilun bana tare hadin gwiwar wani babban kamfanin da ke da hannayen jari a sama da kasashen 20 na nahiyar Afirka.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment