Tuesday, 26 February 2019

Sakamakon Jihohin Borno da Yobe sun gigita 'yan kudu suna ta surfawa 'ya Arewa Ashar

Sakamakon jihohin Yobe da Borno sun tayar dawa da mutanen Kudu, Musamman Inyamurai hankali inda su kaita zagin yanki Arewa da kiransu da sunayen da suka saba na cin zarafi, irin su Almajiri da Malam da kuma fadar cewa wai 'yan Arewan ba su gaji da talauci da kashe-kashen da ake musu ba.Lamarin yayi zafi sosai a shafukan sada zumunta, Musamman a Twitter, inda wasu ke cewa wai ba zasu kara baiwa almajirai 'yan Arewar sadaka ba, wasu kuwa cewa suke idan akayi kisa a arewar ba zasu sake nuna alhini ba tunda dai 'yan arewar sun zabi jam'iyyar APC.

Sun rika kiran 'yan Arewar da jahilai dadai sauransu.

Saidai wannan lamari da alama ba wai akan zabe bane kawai ya tsaya ba, dama can akwai wata azazza, Yobe dai Buharine ya lashe ta sannan da yawa daga cikin kananan hukumomin Borno ma shine yake kan gaba, sannan wai wani abin cewa, shin duk mutanennan ba 'yan Arewa bane? Menene nasu idan 'yan  Arewar suka zabi wani suka kuma ki zaban wani.

Wasu 'yan Arewar sun rika mayar musu da martani. Saidai abinda wannan abu ya kara fito dashi fili shine, idan dai ana maganar mulki na dimokradiyya a kasarnan to dolene fa sai an yi da dan Arewa, sannan zagin da suke wa 'yan Arewa yana kara koresune daga samun damar mulkar kasarnan.

Yawa Alherine, saidai jama'a da kansu su mayar da kansu baya ta hanyar lalaci da ganin cewa su basu isa ba, amma fatan mu a Arewa shine wadatar Ilimi da kuma tashi tsaye wajen neman na kai. 

Duk wanda ya yadda cewa wani mutum zai iya tare mai hanyar arzikinshi to yana da saura a tauhidinshi, dan haka duk wanda zai yi zagin cewa wai talauci wanene ya kawoshi sai ya koma malamai su mai bita.


No comments:

Post a Comment