Tuesday, 26 February 2019

Sakamakon zabe daga yankunan Yarbawa ya batawa wasu 'yan Arewa rai: Saidai a maganar gaskiya ba abin tada hankali bane

Sakamakon jihohin yarbawa, Musamman Legas ya tada hankulan wasu 'yan Arewa tare da bata musu rai inda suka rika rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta suna caccakar kabilar ta yarbawa da butulci.To saidai watakila sun manta da irin tsarin da muke ciki na dimokradiyya da ya baiwa kowane dan kasa 'yancin zabar abinda yake so, koda kuwa dankane, matarka ko wani naka idan yace bazai bi ra'ayinka ba a siyasance bai kamata kaga bakinshi ba ko kuma ka tsaneshi.

Tabbas akwai zafi, lura da irin romon da wadancan yankuna suka kwankwada daga gwamnati me ci amma su saka mata da irin wannan sakamako, saidai abin da ya kamata a duba shine, a karshe dai dan takarar da kake so shine yayi nasara.

Misali a jihar Legas, akwai kabilar Inyamurai da yawa wanda har suna ikirarin cewa Birnin Legas din ya zama gidan kowa, watau ba na yarbawan bane kadai, saboda irin yanda suke ganin sun yi kaka gida a garin.

Kuma kididdiga ta tarihin zaben Najeriya ya nuna cewa Inyamurai dama na jam'iyyar Adawa na PDP ne, haka kuma kididdigar zaben ranar Asabar din data gabata shima ya nuna cewa mafi yawancin kuri'un da PDP ta samu a jihar sun fitone daga yankin da Inyamurai suke zaune wanda har kafafen labarai manya, ciki hadda BBC sun wallafa yanda wasu tsagerun matasan yarbawa suka farwa wadannan yankuna suna musu barazanar su tashi su bar musu gari tunda basa yin ra'ayinsu, wannan ma kadai ya ishi misali da zai wanke yarbawan daga zargi.

Nasan wani zai ce ji wannan mara kishin yana kare su, idan kasan kabilar yarbawa da kyau, to irin wannan abu bazai taba baka mamaki ba, a cikin gida daya, uwa daya uba daya za'a iya samun musulmi, kirista, da wanda ma bashi da addini kuma kaga ana zaman lafiya a kabilar yarbawa. Dan haka basu cika tursasawa akan bin abinda suke so suce kowa sai ya bi irinshi ba.

Ni a ganina wannan ba abin tada hankali bane ko zage-zage da zargi ba, mutanen nan da suka yi takarar shugabancin kasa duka 'yan Arewane to duk ma wanda suka zaba dai mu akaiwa.
Bashir Ahmed.

No comments:

Post a Comment