Monday, 11 February 2019

Sakon Buhari ga ‘yan Najeriya: Ina rokonku ku zabe ni a karo na biyu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki ‘yan Najeriya da su sake bashi dama a karo na biyu domin kammala ayyukan ci gaba da ya faro a kasar nan.


A ‘yar gajeruwar sako na bidiyo da ya yi a yau Lahadi, shugaba Buhari ya bayyana cewa lallai zai tabbata ya cika alkawurran da ya dauka.

‘Yan uwa ‘yan Najeriya

Yanzu fiye da shekara uku kenan da kuka amince mini in ja ragamar mulkin wannan kasa tamu Najeriya.

Tafiyar ba ta zo mana sumul ba, sai dai da ya ke mun mai da hankali sannan mun daura damarar ganin cewa sai mun cimma burin mu na dawo da martabar Najeriya a Idanun mutane ba mu yi kasa-kasa ba wajen ganin an samu nasara a abinda muka sa a gaba. Hakan kuma ya yiwu ne a bisa irin gudunmawar da kuka rika bamu.

Wadannan ayyuka da muka sa a gaba na nan kowa ya san da su sannan ana ganin su. Wasu da dama daga cikin su na nan ana ci gaba da yin su.

Ina rokon ku da ku sake bani dama a karo na biyu domin daukaka darajar Najeriya zuwa mataki na gaba sannan kuma mu taru mu maida Najeriya kasar da dukkan mu za muyi alfahari da. Ba zan yi wasa da goyon baya da kaunar da kuke nuna mini ba. Za mu tattabata mun ci gaba da aiki tukuru domin ci gaban kasar mu sannan mu cika alkawuran da muka dauka.

Nagode.
Premiumtimeshausa.


No comments:

Post a Comment