Sunday, 17 February 2019

Sheikh Bala Lau, Ya Yi Kira Ga Al'ummar Musulmi Da Su Ci Gaba Fa Addu'oin Zaman Lafiya Ga Kasa

Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah wa iqamatis Sunnah (JIBWIS) Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau yayi kira ga Al'ummar Musulmi da suci gaba da addu'oi, da aikata sauran ayyukan ibadu, wadanda suka kunshi yawaita karatun Al'qur'ani da sauran su, domin neman Allah ya zaunar da Naijeriya Lafiya, da kuma ganin anyi wadannan zabubbuka dake tafe a kasar mu ta Naijeriya cikin zaman Lafiya da lumana. 


Shehin Malamin yaci gaba da cewa, "Duk wadanda suke da niyyar ganin ansamu hargitsi a cikin zabubbukan da za'a gabatar, Muna addu'ar Allah ya shirya su in masu shiryuwa ne, in kuma ba masu shiryuwa Bane Allah ya tsare Al'ummar Naijeriya daga sharrin su. 

Kazalika Sheikh Lau ya ummurci mambobin Malisar Zartaswa na JIBWIS, da Shugabannin jihohi da na Malamai, a dukkan matakai tun daga reshe, gunduma, karamar hukuma, jiha a fadin kasar nan,  da suci gaba da addu'o'i da al-qunut dangane da yadda kasa ta samu kanta akan lamarin zabe. 

A karshe Shugaba Bala Lau, ya yi kira ga Jama'a da su yi hakuri Su daure Su fito a sati mai zuwa domin kada kuri'a, ba tare da kosawa ko kasala ba. 

"Muna addu'ar Allah ya zaunar mana kasar mu lafiya, ya bamu shugabanni na gari masu gaskiya da rikon amana,ya kuma kaimu ranar muna masu rai da lafiya. Amin".
Rariya.


No comments:

Post a Comment