Tuesday, 19 February 2019

Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya kare Maganar da Kwankwaso yayi akan malamai

Shehin malamin addinin Islama,Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya kare tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso akan maganar da aka ruwaito cewa yayiwa malamai.Malamin a cikin wani sako daya fitar ta dandalinshi na sada zumunta ya ce idan mutum yayi gwamna a jihar to duk wani babban me laifi ya sanshi haka kuma duk wani malami wanda ke aikata ba daidai ba a boye yasan dashi dan haka idan kace zaka zageshi ku kuma ka fito ka ci mutuncinshi dan baya kan mulki to kaima bazai barka ba zai tona maka asiri.

Malamin yace idan baka so a zageka karka zagi wani.

Ya kuma kara da cewa bai kamata da anzo an gayawa mutum abu ba tare da yayi bincike ba yazo yayi ta yayatashi ba wajan wa'azi da kuma da ya hau kan mumbariba.

No comments:

Post a Comment