Thursday, 14 February 2019

Shin Rahama Sadau da Sadiq Sani Sadiq zasu yi aurene?: Kalli hotunan dake nuna hakan

Wadannan hotunan taurarin fina-finan Hausane, Rahama Sadau da abokin aikinta, Sadik Sani Sadik da ke nuna alamar soyayya a tsakaninsu, wasu daga cikin abokan aikinsu sun saka wadannan hotunan a shafukansu na sada zumunta inda suke musu fatan samun rayuwar aure me kyau.A farkon makonnanne Sadik ya saki wani sako ta shafinshi na Twitter dake cewa so ne kesa mutum ya kara aure koda kuwa yana zaune da iyalinshi lafiya, sakon ya dauki hankulan mutane sosai.

Saidai duk da haka ba za'a cire tsammanin cewa wadannan hotunan na yin wani sabon fim ne ba da ake son fara salonshi da haka dan ya samu karbuwa gurin jama'a ba kamar yanda a kwanakin baya ya faru tsakanin Maryam Booth da Sadik Zazzabi.

Koma dai menene lokaci be bariba.No comments:

Post a Comment