Wednesday, 13 February 2019

Shugaba Buhari da Atiku sun hadu gaba da gaba dan sakawa jarjejeniyar zaman lafiya hannu a karo na biyu

A karo na biyu, shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda shine dan takarar jam'iyyar APC da kuma dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar sun hadu gaba da gaba inda suka sakawa yarjejeniyar zaman lafiya hannu.

'Yan takarar sun sakawa takardar zaman lafiyar hannu ce a dakin taron kasa da kasa dake babban birnin tarayya, Abuja a gaban jama'a da suka hada da, tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, Bishop Mathew Kukah dadai sauransu.No comments:

Post a Comment