Wednesday, 27 February 2019

Shugaba Buhari ya bayyana abinda sabuwar gwamnatinshi zata mayar da hankali akai

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a cikin jawabin da yawa 'yan Najeriya bayan lashe zaben da yayi ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin tashi zata mayar da hankali akan tsaro,  canja fasalin tattalin arziki da kuma yaki da rashawa da cin hanci.Yace sun zuba tubalin hakan kuma zasu mayar da hankali dan ganin ya tabbata.

Yace zai yi kokarin ganin an samu hadin kai a kasar dan tabbatar da cewa babu yankin da zai ga kamar an maidashi saniyar ware.

No comments:

Post a Comment