Saturday, 16 February 2019

Shugaban INEC Munafiki Ne, Jam'iyyar PDP Yakewa Aiki>>In Ji Hon Gudaji Kazaure

Ɗan majalisar wakilai mai wakilatar ƙananan hukumomin Kazaure, Roni, Gwiwa da 'Yan Kwashi ya bayyana cewa shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa wato INEC munafikine kuma ɗan jam'iyyar PDP ne da gangan ya shirya yin hakan domin ya rage ƙwarin guiwar magoya bayan shugaban ƙasa Muhammad Buhari.


Ya ƙara da cewa wasu sun baro garuruwan neman kuɗinsu domin wannan zaɓen, a cikin mutanen nan ba kowane yayi shirin kwanaki da yawa ba, to kaga hakan zai sanya wasu idan sun koma satin ba lalle bane su iya dawowa

Sabo da haka wannan shugaban hukumar ta INEC ya tabbata jam'iyyar PDP yake yiwa aiki, domin su yan PDP dama da kudi aka siye su kuma ko an ɗaga basu da matsalar kuɗi domin suna da Shugaban ɓerayen ƙasar nan .


No comments:

Post a Comment