Sunday, 17 February 2019

Shugaban INEC Ya Amsa Cewar Sanatan APC Ne Ya Yi Kwangilar Kayan Aikin Zabe

A jiya, Asabar, ne shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya amsa cewar sanatan jam’iyyar APC mai wakilta jihar Neja ta gabas, Sanata Mohammed Musa, na daga cikin ‘yan kwangilar hukumar.


Shugaban na INEC ya bayyana haka ne yayin wani taro na ma su ruwa da tsaki da aka yi a cibiyar taro ta kasa da kasa da ke Abuja.

Tun a kwanakin baya ne dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewar INEC ta bayar da kwangilar sayen injinan buga katinan zabe (PVC) ga kamfanin ‘Activate Technologies Limited’ mallakar sanatan jam’iyyar APC, Mohammed Sani Musa.


No comments:

Post a Comment