Wednesday, 20 February 2019

Sojojin Najeriya Sun Yi Ikrarin Gano Wata Makarkashiya Kan Zabe

Rundunar sojojin Najeriya shiyya ta shida da ke birnin Fatakol a jihar Rivers ta ce, ta samu wasu bayanan sirri da suka tabbatar mata cewa wasu ‘yan siyasa sun debo wasu 'yan bangar siyasa daga jihohi daban-daban na yankin Naija Dalta da nufin haifar da tashin hankali a ranar zabe.


A wata sanar da mai magana da yawun rundunar sojoji ta shida, Kanal Aminu Iliyasu, ya rabawa manema labarai jiya, ta ce an gano an bai wa 'yan bangar siyasa makamai da kayan sawa na soja da za su ringa bi rumfunan zabe domin ta da hankalin masu zabe.

Rundunar ta shida ta ce, a shirye ta ke wajen tabbatar da tsaron lafiyar jama’a a ko da yaushe kuma ako wane irin yanayi.

Yayin zabuka na siyasa a yankin Naija Dalta rayukan jama’a na salwanta a ko da yaushe kamar yadda tarihi ya nuna.


No comments:

Post a Comment