Saturday, 9 February 2019

Solari ba ya min adalci>>Isco

Dan wasan tsakiya na Real Madrid Isco, yayi korafin cewa mai horar da su Santiago Solari, baya masa adalci, wajen bashi isasshen lokacin buga wasanni.Tun bayan tabbatar da Solari a matsayin kocin Real Madrid daga watan Nuwamba bara har zuwa shekarar 2021, wasanni uku kawai Isco ya samu damar bugawa ba a matsayin mai dumama benci ba, biyu a gasar Copa Del Rey, daya kuma a gasar cin kofin zakarun Turai, amma a gasar La liga har zuwa wannan lokaci, Solari bai zabi Isco cikin tawagar ‘yan wasansa na farko ba.

Kari kan matsalolin da yake fuskanta, dan wasan tsakiyar na Real Madrid, dumama benci yayi lokacin wasan El Classico na ranar Laraba tsakaninsu da Barcelona, wanda aka tashi 1-1.

Wasan karshe da Isco ya bugawa Real Madrid shi ne wanda suka fafata da Alves a karshen makon da ya gabata, wanda ya shiga a mintuna na 87.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment