Sunday, 10 February 2019

Solkjaer Ya Kafa Sabon Tarihin shekaru 7 A Manchester

 Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester Unted na rikon kwarya, Ole Gunner Soljaer, ya lashe kyautar gwarzon mai koyarwar da babu kamarsa na watan Janairun daya gabata a kasar Ingila. 


Solkjaer ya lashe wannan kyauta ne bayan yajagoranci kungiyar ta United ta lashe wasanni uku a cikin watan na Janairu a jere da suka hada da wasan da kungiyar ta doke Tettenham daci 1-0 a filin wasa na Wembley Har ila yau Solkjaer yajagoranci kungiyar ta lashe wasa da kungiyar Newcastle wanda suka samu nasara daci 1-0 sai kuma wasan da suka doke kungiyar Brighton daci 3-1 a filin wasa na Old Trafford. “Wannan babbar nasara ca ga Manchester United bani kadai ba saboda idan babu kungiyar dab azan samu wanann kyauta ba kuma ina fatan cigaba da samun nasara domin cigaba da lashe irin wadannan kyaututtukan” in ji Solkjaer. 

Ya ci gaba da cewa “Babban abinda nasa a gaba a yanzu shine ganin kungiyar tasamu damar shiga cikin kungiyoyin hudun farko na wanann gasar kuma ina fatan shugabanni da masu koyarwa da ‘yan wasa zasu cigaba da goyamin baya” A karshe Solkjaer ya bayyana cewa ya bayyanawa shugabannin kungiyar burinsa idan har yazama kociyan kungiyar na din-din-din inda yace yana fatan kungiyar zata tabbatar dashi a matsayin kociyanta. 

Rabon da kociyan Manchester United ya lashe kyautar gwarzon mai koyarwa na wata-wata na gasar firimiya tun shekara ta 2012, lokacin tsohin kociyan kungiyar Sir Aled Ferguson wanda ya lashe a watan Oktoba na shekarar.
Leadershipayau.


No comments:

Post a Comment