Thursday, 14 February 2019

Tarayyar Turai ta saka Najeriya da Saudiyya a cikin bakin littafinta

Tarayyar Turai ta saka sunayen Najeriya da Saudiyya a bakin littafinta sakamakon yadda kasashen suka gaza cika ka'idojin yaki da daukar nauyin ta'addanci da fitar kudin haram daga kasashen ko kuma shigar su.


Majalisar Tarayyar Turai ta kuma bayyana karin wasu kasashen duniya 21 da suka gaza cika wadannan ka'idoji kamar haka:

Akwai, Afganistan, American Samoası, Bahamas, Botsvana, Koriya ta Arewa, Itopiya, Gana, Guam, Iran, Iraki, Libiya, Pakistan, Panama, Porto Riko, Samoa, Sri Lanka, Siriya, Trinidad and Tobago, Tunusiya, America Virgin Irelands da Yaman.

Sakamakon haka a yanzu tarayyar Turai za ta sanya idanu sosai kan wadannan kasashe game duk wata mu'amalar kudi da za su yi da kasashe mambobinta.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment