Saturday, 16 February 2019

Tsoron kaye ne ya sa gwamnatin Buhari ta dage zabe>>Atiku

Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da kitsa dage zaben kasar da zummar harzuka 'yan Najeriya.


Sai dai snarwar da Atiku Abubakar ya fitar ranar Asabar ta yi kira ga 'yan kasa da kada su karaya wajen sake fitowa su kada kudi'unsu.

"Sun sani cewa 'yan Najeriya sun yi shirin kayar da su, shi ya sa suka rude suna yin duk abin da za su iya wajen ganin basu sha kaye ba," in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.

Ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta kwashe shekara hudu tana shirin zabe amma sai da aka zo gargara take neman kwancewa 'yan Najeriya zane a kasuwa.


No comments:

Post a Comment