Wednesday, 13 February 2019

UEFA za ta hukunta United da PSG

Hukumar kwallon kafar Turai, Uefa ta tuhumi Manchester United da PSG, bayan kammala wasan farko zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka kara a Old Trafford.


UEFA ta tuhumi United da laifin magoya bayanta da jefa abubuwa cikin fili, ita kuwa PSG ana tuhumar magoya bayanta da jefa abubuwa cikin fili da kunna wuta mai tartsatsi da lalata wasu abubuwan.

An jefi tsohon dan wasan United mai taka-leda a PSG, Angel Di Maria da kwalba, inda aka nuno shi ya dauki kwalbar ya kai bakinsa, daga baya ya jefar da ita.

A ranar 28 ga watan Fabrairu, kwamitin da'a na hukumar zai zauna don sauraren tuhumar don yanke hukunci.

PSG ce ta yi nasara a karawar da ci 2-0 a ranar Talata, kuma Presnel Kimpembe da Kylian Mbappe ne suka ci kwallayen, daga baya aka bai wa Paul Pogba na United jan kati a karawar.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment