Saturday, 9 February 2019

Ummi Zeezee ta mayar da martani akan neman da 'yansanda ke mata

Bayan da tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta fito ta zargi wasu daga cikin abokan aikinta da handame kudin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bada a raba musu, an ruwaito cewa, daya daga cikin wanda ta zarga, Zaharadeen Sani ya kai kararta gurin 'yan sanda har ma suna nemanta ruwa a jallo, Ummin ta mayar da martani akan hakan.Ummi ta mayar da martaninne a yayin da wata ta tabo mata zance a shafinta na dandalin sada zumuntar Instagram, inda tace wa Ummi, Aunty Ummi owner zaharadeen wai ya kai qaranki wai yan sanda na neman ki wai kin bata masu suna bayan barayene su.

Ummin ta bata amsar cewa, Kema sai ki zama yar sanda ai kizo ki tayashi kamani tunda ance miki kama mutum hauka ne abun.

No comments:

Post a Comment