Tuesday, 26 February 2019

'Yan Arewa suna mayar da martanin zagin da 'yan kudu ke musu saboda sun zabi Buhari

Bayan da 'yan kudu, Musamman inyamurai suka sako 'yan Arewa a gaba da zagi a shafin Twitter kan yanda suka zabi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, musamman a jihohin Borno da Yobe, inda suka rika kiran su da sunayen cin mutunci, misali, Jahilai, Almajirai Malam, Aboki dadai sauransu, 'yan Arewar sun mayar da martani.'Yan Arewar yanzu suma sun mayar da martani da wani maudu'i me suna, Iamnorth, wanda a lokacin wannan rubutu, shine na daya wanda yafi daukar hankali a Najeriya.

Da dama 'yan Arewar sun yi amfani da wannan maudu'i inda suka rika bayyana alfahari da kasancewar su sun fito daga yankin da kuma alfahari da yawan da suke dashi da kuma yiwa 'yan kudun shagube akan cewa su basa aikata irin laifukansu.

Ga kadan daga cikin abinda wasu ke cewa akan wancan maudu'i a shafin na Twitter:
No comments:

Post a Comment