Friday, 15 February 2019

'Yan bindiga sun farmaki motocin INEC da ke dauke da kayan zabe

Rahotanni daga jihar Benue a Tarayyar Najeriya na nuni da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kan tawagar motocin jami’an hukumar INEC da ke aikin rarraba kayakin zaben kasar na ranar Asabar 16 ga watan nan.A zantawarsa da manema labarai, Dr Nentawe Yilwatda kwamishinan hukumar ta INEC a Benue, ya ce ‘yan bindigar na sanye ne da kayan Sojoji yayin farmakin kan ayarin wanda ke shirin isar da kayan ga wata karamar hukuma da ke jihar.

A cewar Dr Yilwatda, ayarin motocin da ‘yan bindigar suka farmaka basa dauke da muhimman kayakin zabe.

Kwamishinan zaben bai sanar da ko an rasa rai yayin farmakin ba, haka zalika bai bayyana ko ‘yan bindigar sun kwace kayakin zaben ba ko a a ba.

Kwanaki biyu dai kacal ya rage a gudanar da babban zaben Najeriyar wanda za a kara tsakanin 'yan takara fiye da 70, amma ana ganin mafiya jan hankali bai wuce tsakanin Jam'iyya mai mulki ta APC da kuma babbar Jam'iyyar adawa ta PDP ba.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment