Saturday, 9 February 2019

'Yan kwallon kafa 10 da suka fi karbar albashi me tsoka

Baya ga daukaka da mutum ke samu a harkar kwallon kafa abu na biyu dake kara daukar hankali shine irin makudan kudaden da ake biyan 'yan wasa ta yanda zaka ga ana biyan dan kwallo miliyoyin daloli a cikin wata daya.



Kafar watsa labarai ta L'Equipe's dake kasar Faransa ta fitar da rahotonta na shekara-shekara da ta saba fitarwa akan 'yan kwallon kafa 10 dake wasa a turai da suka fi karbar Albashi me tsoka.

Dan kwallon kafar kasar Argentina dake bugawa kungiyar Barcelona, Lionel Messi ne kan gaba inda yake daukar zunzurutun kudi har Yuro miliyan 7.3 a duk wata sannan sai dan kwallon kafar kasar Portual me bugawa kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo wanda shi kuma ke daukar Yuro miliyan 4.1 duk wata, na uku shine dan kwallon kafar kasar Faransa me bugawa kungiyar Atletico Madrid wasa, Antoine Griezmann da shi kuma ke daukar Yuro 2.9 duk wata.

Ga jadawalin 'yan wasan goma da suka fi albashi a Duniya.

1. Lionel Messi – £7.3million

2. Cristiano Ronaldo – £4.1million

3. Antoine Griezmann – £2.9million

4. Neymar – £2.7million

5. Luis Suarez – £2.5million

6. Gareth Bale – £2.2million

7. Philippe Coutinho – £2million

8. Alexis Sanchez – £2million

9. Kylian Mbappe – £1.5million

10. Mesut Ozil – £1.4million 

No comments:

Post a Comment