Tuesday, 12 February 2019

Yar Shekara 14 Ta Datse Al'aurar Wani Mutum Da Ya So Yi Mata Fyade A Katsina

Wata yarinya 'yar shekara 14 ta datse al'aurar wani mutum me suna Bashir Ya'u da ya yi yunkurin yi mata fyade a kauyen Yargasa na jihar Katsina. 


Jaridar Katsina Post ta yi rahoton cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ce ta bayyana lamarin a sa'ilin da ta gurfanar da mutumin dan shekara 30 a gaban kuliya.

Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa ta samu rahoton bayan da wanda ake zargin ya kai kansa babban asibitin Kankara na jihar Katsina domi a yi masa magani.

Ta bayyana wa kuliya cewa wanda ake zargi da laifin fyaden ya ja yarinyar 'yar shekara 14 zuwa wani kango a kusa da su inda yai ta yi mata fyade.

Rundunar ta kara da fadin cewa da yarinyar ta ga ba sarki sai Allah sai ta zaro reza inda nan take ta datse masa  al'aura.

Rundunar 'yan sanda ta tuhumi ya'u da laifin aikata fyade wanda ya saba wa sashe na 283 na kundin laifuka da hukuncinsu na kundin Final Kod.

An umarcin Bashir Ya'u, wanda a yanzu yake karkashin beli, da ya gurfana a gaban babbar kotun majistare ta Katsina, karkashin Mai Shari'a Fadila Dikko, ran 4 ga watan Afrilu, 2019, domin fuskantar tuhuma.  

Dan sandan da ya gurfanar da wanda ake karar, Insifekta Sani Ado, ya bayyana wa kotun cewa sun kammala dukkan bincike game da takaddamar.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment