Wednesday, 13 February 2019

Yaran Shugaban APC Na Jihar Kano Sun Kuma Kai Wa Abba K Yusuf Farmaki>>Sanusi Bature

An kai farmaki gidan iyayen dan takarar kujerar gwamnan Kano karkashin tutar jam'iyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf, hadiminsa Mustapha Ibrahim Chigari da kuma sauran makwaftansu da misalin karfe dayan ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu, 2019, a unguwar Gwale da ke kwaryar birnin Kano. 


Ba a samu salwantar rai a farmakin ba amma wasu mutane mara sa yawa sun samu raunuka, sannan 'yan daban wadanda aka yi imanin suna karkashin umarnin shugaban jam'iyar APC, Abdullahi Abbas, sun kuma yi awon gaba da wasu kayayyaki masu daraja. 

Maharan, wadanda wani shahararren jagoran 'yan daban siyasa mai suna Dandaba ya jagoranta, da Sarki, shi ma jagoran 'yan daba kuma mukusanci ga Abdullahi Abbas, sun samu goyon bayan wasu 'yan sandan da ke tare da shugaban jam'iyar APC gurin gabatar da tarin hare-haren da ake kaiwa a unguwar Chiranchi, karamar hukumar Gwale, jihar Kano.

Ba a amsa dukkan kiraye-kirayen da aka dinga yi wa ofishin 'yan sandan Gwale a lokacin da ake gabatar da farmakin ba, wanda hakan ya tona asirin bambancin da jami'an tsaron yankin suke nunawa.

Muna so mu fito fili mu bayyana cewa, matukar jami'an tsaro suka gaza gabatar da muhimmin aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin al'umma, to kare kai ba laifi ba ne a addinin Musulunci da dokar Nijeriya.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment