Tuesday, 19 February 2019

Yarima ba shi da niyyar sayen Manchester United>>Saudiya

Gwamnatin Saudiya ta musanta cewa, Yarima mai jran gadon sarautar kasar Muhammad Bin Salman, na shirye-shiryen sayen kungiyar Manchester United.Rahoton cewa Muhammad Bin Salman zai sayi United ya bulla ne bayan taron da ya gudana tsakaninsa da wasu shugabannin kungiyar.

Sai dai ministan yada labaran Saudiya Turki al-Shabanah, ya ce yayin taron shugabanin Manchester United, sun tattauna da Yarima mai jiran gado ne kan batutuwan da suka danganci daukar nauyin kungiyar a wasu fannoni.

A jiya Lahadi, jaridar Sun da ke Birtaniya, ta wallafa rahoton Yarima Muhammad bin Salman, yayi tayin biyan dala biliyan 4 da miliyan 900, domin sayen kungiyar Manchester United.

Jaridar ta rawaito cewa tun a watan Oktoba na 2018 Yariman na Saudiya ya gabatar da tayin nasa.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment