Thursday, 14 February 2019

Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado ya hau rufin dakin Ka'aba

Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado Muhammad bin Salman ya hau doron dakin Ka'aba a lokacin da ya ziyarci garin Makka Mai Girma.


Rahotanni sun ce, Yariman ya ziyarci garin na Makka domin duba sabbin aiyukan da ake gudanarwa a Dakin Allah Mai Tsarki.

Yariman da ya halarci wanke Dakin Ka'aba da aka saba yi tare da jami'an tsaro 600 dake kare shi ya fara sumbatar Hajarul Aswad inda daga nan kuma ya hau matattakalar tare da shiga cikin dakin Ka'aba.

Yarima bin Salman ya yi Sallah a cikin Ka'aba inda ya dauki wani tsumma tare da yin goge-goge, sannan kuma sai ya hau saman rufin Dakin Mai Tsarki wanda abu ne da ba a saba gani ba.

Hawan Yariman saman Dakin Ka'aba ya janyo ka ce na ce a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

An samu tarihin cewar daga cikin Halifofin Daular Abbasiyya Abu Ja'afar Al-Mansur ya taba hawa rufin Dakin.

A yanzu dai ma'aikata na hawa saman Dakin don tsaftace shi a lokacin da aka yi ruwan sama ko kuma za a sauya rigarsa.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment