Thursday, 14 February 2019

Za a dakatar da Bale buga wasanni

Mahukuntan gasar La Liga sun bukaci hukumar kwallon kafar Spaniya (RFEF) ta hukunta Gareth Bale, sakamakon yadda ya yi murnar cin kwallo a karawa da Atletico Madrid.


Bale dan kwallon tawagar Wales ya yi nuni da hannayensa a murnar kwallo na uku da ya ci wa Real Madrid kuma na 100 jumulla, wanda hakan ya harzuka magoya bayan Atletico.

Bale din ya yi wata alama da hannuwansa, wadda batanci ce a Spaniya, kuma hakan ne ya harzuka magoya bayan Atletico Madrid.

Cikin hukuncin da La Liga ke sa ran a dauka kan Bale ya hada da dakatarwa wasa hudu zuwa 12.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment