Friday, 15 February 2019

"Za mu durkusar da arzikin Najeriya muddin Buhari ya lashe zabe">>Inji tsagerun Naija Delta

‘Yan tawayen Niger Delta sun yi barazanar durkusar da tattalin arzikin Najeriya muddin aka sake zaben shugaba Muhammadu Buhari a wa’adi na biyu a zaben 2019.‘Yan tawayen sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Alhamis, kasa da sa’oi’i 42 a gudanar da zaben shugabancin kasar.

‘Yan tawayen sun ce, suna fatan kawo karshen mulkin Buhari ta hanyar zabar babban mai adawa da shi na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da suka ce suna goyon baya.

Mayakan Niger Delta Avengers sun taka rawa a wasu rikice-rikicen da suka taimaka wa wajen tsindimar Najeriya cikin matsalar koma-bayan tattalin arziki a shekarar 2016.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment