Monday, 11 February 2019

Ziyarar Atiku fadar sarkin Kano: Karanta abinda sarkin ya gayamai

Wadannan hotunan yanda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya kaiwa sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ziyara a fadarshi jiya yayin yakin neman zabenshi da yaje yi a jihar.Jawabin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi ll Yayin Zuwan Mai Girma Wazirin Adamawa Fadarsa A Yau Lahadi 10/02/2019. 

Daga Sa'adatu Baba Ahmad

“Duk da alakar wannan gida ta mutuntawa ga wadannan ‘yan takara, muna nan a matsayinmu na iyayen al’umma ko me ya taso wajenmu za a zo don haka kowa namu ne. Muna kira ga jama’a da su fito su karbi katinansu na zabe don su samu damar zaben wadanda suke so kuma muna fatan a gudanar da zabe cikin lumana. Muna yi wa maigirma Wazirin Adamawa da maigirma Senator Rabi’u Musa Kwankwaso da ‘yan tawagarsu maraba da zuwa kuma muna fatan su yi taro lafiya su tashi lafiya, Allah ya bamu lafiya da zama lafiya” Allah ya taimaki sarki ✊🏽.


No comments:

Post a Comment