Monday, 11 February 2019

Zuwan Buhari Zamfara: Na Yi Mamaki Da Bai Jajantawa Al'ummar Zamfara Ba Tare Da Kin Yin Magana Kan Halin Da Suke Ciki

A baya ana ta cece-kucen zuwan shugaba Muhammadu Buhari a Zamfara akan yana kila wa kala, sai dai daga baya ya yanke shawarar zuwa.


Abun farin ciki ne yadda 'yan Zamfara suka yi kokarin fitowa har suka tarbi shugaba Buhari duk da halin kunci na rashin tsaro da satar mutane da muke fama da shi.

Alhamdulillahi an yi wannan taro lafiya, an kare lafiya,  sai dai mu koma kan batuna na farko wato zuwan shugaba Muhammadu Buhari da ya ba mu mamaki.

Mamakin a nan shine kowa dai ya san halin da Zamfara ke ciki da rashin tsaro da satar mutane, shugaba Buhari ya zo daidai lokacin da ba'a shige mako guda da yin wani mummunan kisan gilla a kauyukan Bakenawa da Gurbin Bore, inda suka kashe mutane 11 bayan kwana uku kuma suka dawo suka kashe mutane 14. 

Abun mamaki shine shugaba Muhammadu Buhari bai yi jaje ba ga wannan kashe kashen ba, har ma bai tabo halin da Zamfara ta tsinci kanta ba,  gaskiya ba mu ji dadin hakan ba matuka, duk da bamu saurin zargin shugaba Buhari ba kan kasa cewa uffan game da tsaro, domin zai iya yiyuwa wakilan da yakamata su kai kokarin mu gare shi.

Wakilai da za su iya zuwa ga shugaba Buhari su fada mashi sun gaza, Dan haka yakamata Dan girman Allah wakilan da yakamata su fadawa shugaba Buhari game da matsalar tsaro suyi kokarin fada mashi! 

'Yan ta'adda sun karya mutanen Zamfara, sun hana mu kasuwan Ci, Amma da yardar Allah an kusa kawo karshen su! 

Ina rokon Allah ya bamu zaman lafiya mai dorewa da wadatuwar arzirta, Sannan Ina fatar wannan sakon ya kai ga shugaba Muhammadu Buhari.
Daga Ibrahim Rabilu Tsafe.


No comments:

Post a Comment