Saturday, 30 March 2019

A Baya Na Tsani Musulunci Amma Yanzu Ba Ni Da Addinin Da Ya Fi Shi>>Tsohon Sojan Amurka Da Ya Musulunta

Wani tsohon sojin Amurka mai suna Richard McKinney, wanda shahara haikan wajen nuna makauniyar kyama ga Musulunci da Musulmai, ya karbi kalmar shahada tare da zama limami a masallacin da ya kuduri kai wa harin ta'addanci ta hanyar amfani da bama-baman da ya samar da karan kansa.


A daidai lokacin da hankali duniya ga baki daya ya karkata kan hare-haren ta'addancin da suka rutsa da rayukan Musulmai 50 a kasar New Zealan,labarin wannan sojan na Amurka wanda ya makance wajen kyamar Musulunci da Musulmai ya girgiza jama'a matuka gaya.

A cewar kafafan yada labaran yankin Indianan kasar Amurka,wani tsohon soja wadanda ya share shekaru da dama a yankunan da suka hada  Gabas ta Tsakiya, Somali, Filipins da kuma Latin Amurka, ya dawo kasarsa da makauniyar kyamar Musulunci da Musulmai,wadanda ya lashi takobin ganin bayansu ko ta halin kaka.

Sojan ya ce a 'yan kwanakin da suka gabata,ya dinka shirye-shiryen yin raga-raga da masallatan Muncie da kuma kashen Musulmai masu dumbin yawa ta hanyar amfani da bama-baman da ya samar da karan kansa

McKinney ya kara da cewa, "A gaskiya a lokacin da nake wadannan shirye-shiryen, ban damu da hukuncin da za yanke mun ba.Ni dai bukatata in ga bayan Musulmai ko ta halin kaka.Amma wata rana, kankanuwar 'yata ta ba ni labarin tufafin da wata kawayarta Musulma ta saka a makaranta.Abin da yasa na garzaya cibiyar Islama da nufin ganawa da Musulmai

Ya ci gaba da cewa, "Zuwa cibiyar Islamar ke da wuya, Musulman da ke wurin,suka karanta mun wasu daga cikin ayoyin Al Kur'ani mai tsarki.Tun a wannan ranar,na kwashe makwanni 8 ina zuwa a wannan cibiyar ta Islama.Saboda maganganunsu sun yi tasiri a zuciyata.Na samu amsoshin dukannin tambayoyin suka dade suna kai-kawo a kwakwalwata.Sai kwatsam, wata rana na yanke shawarar karbar kalmar shahada.Na karbi Islama,addinin manyan makiyana.

McKinney ya ce, bayan ya musulunta, ya zama abin kwaikwayo ga mutanen yankin Indiana da dama,inda a yanzu haka shi ne shugaban masallacin da ya kuduri kai wa hari ta'addanci.Ina ci gaba bada gudunmowata don ganin an kau da dukannin karyace-karyace da kuma tunace-tunace marasa tushe da asali da ake ci gaba da yadawa kan Musulunci da kuma Musulmai. Ina iya kokarina don ganin na kare Musulunci da kuma Musulman da ke a wannan yankin.
Rariya.
No comments:

Post a Comment