Sunday, 31 March 2019

A mahangar Messi: Ronaldo baya cikin 'yan kwallo 5 mafi shahara a Duniya


Lionel Messi and Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo be shiga cikin jerin 'yan wasa 5 da suka fi shahara a Duniya ba a mahangar babban abokin takararshi, lionel Messi yayin da aka tambayeshi wane dan wasa yake ganin yafi yin fice da iya kwallo a Duniya?

Messi yace, Kylian MbappeNeymarEden HazardLuis Suarez, da Sergio Aguero ne 'yan wasan da suka fi shahara a Duniya.
Ya bayyana hakane a wata hira da wani gidan rediyo yayi dashi.

Duk da cewa, Messi be saka Ronaldo cikin 'yan wasa biyar da yake ganin sun fi shahara a Duniyar kwallo ba amma ya yabeshi inda yace, abin jin dadine kasan cewar Ronaldo a gasar Laliga saboda irin daukar hankalin da hakan ya jawo.

Messi ya kara da cewa banda ni dashi, 'yan kwallon mafi shara a Duniya sune MbappeHazardSuarezAguero da Neymar.

No comments:

Post a Comment