Friday, 15 March 2019

Abba Gida-Gida a Landan::Za mu tabbatar da nasarar PDP a Kano>>Yusuf Bakin-Zuwo

Babban jigo a siyasar Kwankwasiyya kuma fitaccen matashin dan kasuwar kasa da kasa Alhaji Yusuf Yunusa Bakin- Zuwo ya bayyana cewar al'ummar Kano da ke muradin samun ingantaccen mulki nagari za su sake tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano da gagarumar nasara. A sakon fatar alheri da ya aikowa Rariya daga Birnin Landon, Yusuf Bakin- Zuwo wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen ganin jagoran Kwankwasiyya na Kasa, Sanata Rabi'u Kwankwaso ya sake kafa Gwamnatin Kano ya bayyana cewar shugabancin gaskiya da adalci, wanzar da zaman lafiya da ci-gaban jama'a da Kwankwaso ya gudanar a Kano ne dalilin da yasa Kanawa suka sake bashi cikakken goyon baya. 

Ya ce "Tabbas hakika a wannan zaben Kanawa sun nunawa duniya cewar siyasar da suke yi siyasa ce ta kishi, sanin ya kamata da hangen nesa a kokarin ciyar da jama'a a gaba wanda a kan hakan ne al'ummar Kano maza da mata suka jagoranci nunawa Ganduje kofar fita daga Fadar Mulki a hobbasar samar da sauyi da canji mai ma'ana." In ji Bakin -Zuwo wanda ya kara da cewar 'yan Nijeriya mazauna Ingila na yi wa Abba Gida-Gida fatar alherin zama zababben Gwamnan Kano a zabe zagaye na biyu da za a gudanar.
Rariya.


No comments:

Post a Comment