Saturday, 16 March 2019

Abba Kyarine yasa mu fadi sunan Saraki a matsayin me daukar nauyinmu>>'Yan fashin Offa

'Yan fashinnan da ake zargi da sata a bankunan Offa na jihar Kwara wanda suka bayyana sunan Sanata Bukola Saraki a matsayin daya daga cikin masu daukar nauyinsu sun bayyanawa babbar kotun Ilori cewa shugaban fannin bincike na hukumar 'yansandan DCP Abba Kyarine ya tilasta musu su saka sunan Saraki a matsayin wanda ke daukar nauyinsu.Wadanda ake zargin, Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye da Adeola Abraham sun bayyanawa Kotun a zamanta na jiya cewa, 'yansanda sun tursasasu ta karfin tsiya dan matsar bayanai daga bakunansu.

Akinnibosun ya bayyanawa kotun cewa, Abba Kyari yace mai ya fadi sunan Saraki a matsayin wanda ke basu bindigun aiki amma sai yaki yadda ganin cewa zai iya saka rayuwarshi cikin hadari.

Ya ci gaba da cewa Abba Kyari ya mai alkawarin bashi lada me tsoka idan ya fadi sunan Saraki sannan kuma zasu sakeshi amma duk da haka sai yaki yarda, ganin haka sai suka sa aka mayar dashi aka kulle cikin halin takura.

Ya kara da cewa, babban wanda ake zargi da laifin fashin wani tsohon dan sandane da aka sallama daga aiki, Michael Adikwu kuma a gabansu dan sanda me bincike, Vincent wanda akewa lakabi da me horo ya harbeshi da bindiga saboda yaki amincewa ya sakasu cikin wanda aka yi aika-aikar dasu.

A karshe dai me shari'a Halimat Salman ta dake sauraron karar sai ranar 25 ga watan Maris dinnan da muke ciki, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment