Sunday, 31 March 2019

Adam A. Zango ya mayarwa da masu cece-kuce akan saka hotunan matar da zai aura da yake yi a shafunashi martani

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya mayar da martani ga masu cece-kuce akan saka hotunan matar da zai aura da yake yi a shafukanshi na sada zumunta, yace shi badan ya bakantawa kowa yake hakan ba yana yi ne dan tana faranta mishi rai sannan zuciyarta tafi fuskarta kyau.Wani abu daya kara fitowa fili a wannan rubutu da Adamun yayi a shafinshi na Facebook shine, jita-jitar da ake yi cewa har an riga an daura aurenshi da wannan masoyiyar tashi ba gaskiya bane.

Ga dai abinda ya rubuta kamar haka:

"Idan ka karbi dukanin jarabtar da ALLAH ya qaddara maka, daga karshe sai yayi maka sakamako mai kyau. Nasan cewa duk wanda yaga hoton soffy zaice kyakykyawa ce. Sai dai kash zuciyarta yafi fuskarta kyau. Sannan bana posting hoton matar da zan aura don bakantawa wata ba kamar yadda wasu ke tsammani. Ina posting dinta ne don ta kasance mai faranta min rai tun kafin ta shigo gidana. YOU PEOPLE SHOULD MIND YOUR OWN BUSINESS PLEASE. IF YOU DON'T WANNA SEE ME HAPPY THEN GET THE F**CK OUT OF MY ACCOUNT."

No comments:

Post a Comment