Saturday, 9 March 2019

Akuya ta zama magajiyar gari

A karo na farko a tarihin kasar Amurka an zabi wata akuya mai suna "Lincoln" a matsayin magajiyar garin  "Fair Haven" da ke yankin Vermont.


A cewar kafar yada labarai ta Associated Press (AP ),an zabi akuyar a matsayin magajiyar gari ta musamman a garin "Fair Haven" wanda al'umarsa ta haura kimanin mutum dubu 2,500.

"Lincoln" za ta rike wannan mukamin a tsawon shekaru biyu tare da jagorantar da muhimman aiyuka da bukukuwan garin.

A cewar bayanan da shugaban garin "Fair Haven", Joe Gunter yayi a wani taron manema labarai, an dauki matakin zabar akuyar a matsayin magajiyar gari saboda an share lokacin mai tsawo ba tare wani ya rike wannan mukamin ba.

Gunter ya kara da cewa, kimanin dabbobin 16 ne suka tsaya a takarar zaben magajin garin da aka shirya a garin nasu,inda kowace dabba ta biya dalar Amurka $5 don gwada sa'arta.

"Lincoln" mai shekaru 3 da haihuwa ce ta lashe wannan zaben ta hanyar samun kuri'u 13 a cikin 53 da aka jefa.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment