Friday, 15 March 2019

Ali Nuhu na murnar cika shekaru 16 da yin aure da kuma murnar zagayowar ranar haihuwarshi

Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu,Sarki yayi murnar cika shekaru 16 da yin aure tare da matarshi, Maimunatu. Yayi fatan Allah ya basu zaman lafiya da karin dankon soyayya, sannan ya roki 'yan uwa da abokan arziki da a sakasu a addu'a.
Ali Nuhu na da 'ya'ya biyu,Ahmad da Fatima, muna fatan Allah ya kara dankon soyayya.

Haka Ali Nuhu na murnar zagayowar ranar haihuwarshi, muna tayashi murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.

No comments:

Post a Comment