Monday, 11 March 2019

An dawo da bayyana sakamakon zaben gwamna a Kano saidai an hana 'yan jarida dauka, sannan 'yansanda sun yi harbi a iska

An dawo da bayyana sakamakon zaben gwamna a jihar Kano bayan da kwamishinan zaben jihar a baya ya bayyana cewa an yayyaga sakamakon karamar hukumar Nasarawa waddda ita kafai ce ta rage ba'a bayyana ba a jihar.Saidai BBC ta bayyana cewa an hana watsa abinda ke faruwa a dakin tattara sakamakon zaben.

Kwamishinan zaben, Risikuwa Shehu ya bayyana cewa duk da an yaga sakamakon zaben Nasarawar amma zasu yi amfani da dabari wajan zamun sakamakon Nasarawar kai tsaye daga mazabu.

Haka kuma rahoton Punch yace 'yansanda a hedikwatar tattara sakamkon sun yi harbin Iska, sun kara da cewa ba'a san dalilin da yasa aka yi harbin ba.

Amma an karo jawan jami'an tsaro a gurin tatara sakamakon, kuma kwamishinan 'yan sanda na jihar, Muhammad Wakili ya gana da gwamishinan zaben jihar, Risikuwa Shehu.

No comments:

Post a Comment