Saturday, 9 March 2019

An fi kyamar Musulmai a Amurka

Sakamakon wani zurfaffen binciken da aka yi a baya-bayan nan ya nuna cewa,Musulmai sun fi dukannin mabiya sauran addinan da ke Amurka fuskantar muzgunawa da kuma makauniyar kyama.


Daya daga cikin manya-manyan jaridun Amurka,The Hill tare da hadin gwiwar HarrisX,cibiyar nazari kan yanayi da kuma zamantakewar al'uma ne, suka gudanar da wannan binciken da nufin gano addinan da aka fi nuna wa kyama a kasar.

Binciken wanda aka gudanar tsakanin ranakun 1 da kuma 2 ga watan Maris na bana, ya nuna cewa kashi 85 cikin dari na mutane dubu 1003 da aka nemi su bada ra'ayinsu kan wadanda suka fi fuskantar tsangwama a Amurka,sun bayyana cewa,Musulmai ne.

Wannan binciken wanda aka yi a washegarin wasu kalaman da Ilhan Omar ,Musulma daya tak wacce  ke wakiltar yankin Minnesotan Amurka a majalisar dokokin kasar,ta furta kan  Isra'ilai ya haifar da da mai ido.

Yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan bayanan na Misis Omar,babbar hukumar da ke kula da harkokin da suka danganci Musulunci a Amurka (CAIR),wannan binciken da aka sabunta ya nuna cewa,kyamar Musulunci da Musulmai ta yi kamar kamari a kasar.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment