Sunday, 10 March 2019

An fi yin magudi a zaben gwamnatin Buhari>>PDP

Babbar jam'iyya hamayya a Najeriya PDP ta zargi gwamnatin APC da yin amfani da karfi domin lashe zaben gwamnoni.


Wasu jerin sakwanni da jam'iyyar ta wallafa a Twitter, PDP ta yi Allah Wadai da abin da ta kira "yin amfani da karfin soji da kamawa da harbe 'yan adawa bisa umurnin shugaba Buhari"

PDP ta ce a tarihin Najeriya ba a taba zaben da aka zubar da jini ba da tashin hankali da kuma magudi kamar zaben 2019 na zamanin gwamnatin Buhari da APC ba.


Zuwa yanzu dai babu wani martani da ya fito daga fadar shugaban kasa ko jam'iyyar APC game da wannan zargin na PDP.

Daga cikin zargin na PDP ta ce a jihohin Rivers da Akwa-Ibom da Cross River da Delta da Bayelsa da Kogi da Benue da Imo da Abia da Ebonyi, sojoji sun hada baki da 'yan daba suka sace kayan zabe tare rubuta sakamakon karya da ya ba 'yan takarar APC nasara.

Ba zai zo da mamaki ba idan PDP ta yi watsi da sakamakon gwamnoni bayan ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar tun da farko.

Jam'iyyar ta ce za ta garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon da ya tabbatar da shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment