Saturday, 9 March 2019

An Guntule Masa Kunne Sakamakon Rikicin Siyasa

Wannan bawan Allah da kuke gani matashi ne dan unguwar Nasarawa Jahun da ke garin Bauchi, matasa 'yan Sara suka masu fadar siyasa ne suka fille masa kunnensa. Bayan zaben shugaban Kasa a kwanakin baya.


Tsautsayin ta riske shi ne a lokacin da ya fito kallon fadar siyasa a tsakanin 'yan bangar siyasa. 

Bayan saransa da aka yi a sassan jikinsa an fille masa kunne, laifinsa ya fito kallon fadar siyasa.

To, shawarata gare ku, shine a duk lokacin da Kuka ga ana fadar siyasa don Allah ku adana kawukanku a cikin gidajenku domin gudun tsautsayi, Allah Kuma ya kare mu, amma dai kiyayewa na da kyau.
Daga Khalid Idris Doya.
Rariya.


No comments:

Post a Comment