Saturday, 9 March 2019

An kama mota makare da kudi a Sokoto

Gabanin zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi, an kama wata mota makare da kudi a jihar Sokoto.


Hukumar yaki da cin hanci da zagon kasa ta EFCC tare da jami'an tsaro ne suka kama mota kirar Jeep makare da kudi da ake zargin za a yi amfani da su ne wajen sayen kuri'u a jihar Sokoto.


An kama motar mai lamba ABC 924 LU a kan titin Garba Duba da ke Sokoto a daren Juma'a da karfe 10:30 inda aka kai motar hedikwatar 'yan sanda a jihar Sokoto.

Daga nan ne aka fito da buhunhunan kudi domin yin bincike.

An yi ta kokarin jin ta bakin kakakin 'yan sanda kan lamarin, yayin da jami'an tsaron suka hana daukar hotunan kudin.

Sai dai ana sa rai hukumar 'yan sanda za ta yi taron manema labarai a yau Asabar kan lamarin.

'Yan kwanaki kafin zaben shugaban kasa ne wani hoton bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta na wani jirgin sama makare da kudi a wani filin jirgin.

Hakan kuma ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu 'yan Najeriya suka rika ganin cewa kudin sayen kuri'u ne.

Haka kuma, an samu rahotannin sayen kuri'u a wasu jihohi inda aka rika raba kudi, da silifas da maganin sauro da wasu kayan masarufi.

Irin wannan rabon kudi da kayyyaki a lokacin zabe dai abu ne da INEC ta haramta, sai dai duk da haka a kan sami wuraren da ake yi.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment