Friday, 29 March 2019

An yi taron nuna Alhini kan kisan da dan ta'adda yawa musulmi 50 a New Zealand: Daya daga cikin wanda ya tsira daga harin amma matarshi ta mutu yace ya yafewa maharin: An gano marin ya nuna alamun kai harin amma 'yansanda basu dauki matakiba


A view of the crowd, including a young boy on his father's shoulders, in Hagley Park on March 29
An yi taron tunawa da mutane 50 da suka rasa rayukansu a harin ta'addanci da wani dan rajin kare hakkin farar fata yakai a birnin Christchurch na kasar New Zealand. Taron tunawa da girmama mamatan wanda aka yi a wani fili dake kusa da masallatan da aka kai harin, ya samu halartar mutane sama da dubu 20.

 Firaiministar kasar, Jacinda Ardern ta halarci gurin inda ta gabatar da jawabi, tace suna da aikin mayar da kasasu irin kasar da suke burin ta zama sannan sun san cewa akwai matsalolin kiyayya da tsoro a kasarsu amma ya kamata su zama kasar da zata samar da hanyoyin warwaresu.

Wasu shuwagabannin kasashen Duniya sun samu halartar taron na yau, sannan shahararren mawakinnan, Cat Stevens wanda ya musulunta ya kuma canja sunanshi zuwa Yusuf Islam ya halarci gurin in har yayi waka.
Cat Stevens playing guitar on stage at a memorial service for victims of the shooting on 29 March
An kira sunayen mutanen 50 da suka rasu a harin a wajan taron kuma da dama daga cikin danginsu sun halarta.
Two girls crying in the crowd at the remembrance service for victims of the mosque attacks
Wadannan wasu 'yan kasarne dake kuka a yayin da ake rera taken kasar na New Zealand.

Farid Ahmed, a survicor of the Christchurch shooting, waving to the crowd at the remembrance service on March 29
Daya daga cikin wanda ya tsira daga harin, Farid Ahmad kenan wanda kuma matarshi ta rasa ranta a harin. Ya bayyana cewa ya yafewa maharin domin baya son zama da zuciyar da zata rika tafasa a koda yaushe, yana son samun zuciyar da ke cike da soyayya, kula, da tausai.
Saidai kuma wani sabon rahoto da kafar ABC ta wallafa na nuna cewa kwanaki kadan kamin maharin ya kai harin da ya kai, ya saka hoton daya daga cikin masallatan daya kashe mutane, watau masallacin Noor a shafinshi na Facebook inda ya rika sanya wasu kalamai na kiyayya ga musulunci.

Abin tambaya shine ya akai jami'an tsaro kokuma wasu masu sa ido akan harkar tsaro basu ga wannan abin da maharin yayi ba.

ABC tace ta tuntubi 'yansandan kasar akan wannan lamari ko sun san da hotunan da maharin ya saka a shafinshi na Facebook kwanaki kadan kamin hatin da ya kai?

Saidai sunce suna bincikene akan abubuwa da dama da suka danganci harin bawai wani fanni guda daya ba.


No comments:

Post a Comment