Wednesday, 6 March 2019

APC ba zata ji dadin mulkin shekaru hudunnan ba, a gantalin zuwa kotu zai kare>>Ummi Zeezee

Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee wadda tana daya daga cikin na gaba-gaba wajan tallata dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da yayi rashin nasara a zaben shugaban kasar da ya gabata, Atiku Abubakar, ta dawo daga jiyyar da ta yi bayan kwanaki biyu ba'a ji ta ba a shafinta na Instagram.Ummi ta bayyana cewa maganar siyasa ta wuce tunda shugaba Buhari ya ci zabe, saidai wata ta ce mata bata wuce ba tunda za'a hadu a kotu.

Ummi ta amsa da cewa tabbas hakane dan ba zasu ji dadin mulkinnan na shekaru hudu da ya rage musu ba dan a gantalin zuwa kotu zai kare.

No comments:

Post a Comment