Sunday, 24 March 2019

APC ta ba PDP tazara a zaben da aka sake a Kano Sakamakon zaben gwamna a Kano

Zuwa yanzu sakamakon zaben da aka sake bai yi wa jam'iyyar PDP da ke son kwace mulki daga hannun APC dadi ba.


A zaben 9 ga watan Maris da aka gudanar PDP ce kan gaba da tazarar kuri'a sama da dubu 26.

Amma yanzu APC ta samu jimillar kuri'u 34,969 yayin da PDP ta samu jimilla 6,602 na kuri'un da aka bayyana daga mazabun kananan hukumomi 26 da aka sake zaben gwamnan Kano.

Yanzu APC ta datse tazarar da ta ba PDP idan aka hada da sakamakon zaben farko da kuma na kananan hukumomin da aka bayyana kawo yanzu.

Kananan hukumomi biyu suka rage a kammala bayyana sakamakon zaben, wato Kibiya da Nassarawa.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment