Thursday, 7 March 2019

APC ta mayarwa da Obasanjo martani kan cewa da yayi shi Ogan Buharine

A lokacin da yake bikin murnar zagayowar ranar haihuwarshi, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ba zai daina sukar gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba saboda shi ogan Buharinne, da alama maganar ba tawa jam'iyyar APC dadi ba, dan kuwa ta mayar da martani.Kakakin kwamitin yakin neman zaben Buharin, Barista, Festus Keyamo ya mayarwa da Obasanjon martani a wani sako da ya fitar ta shafinshi na Twitter inda yace, Dan kawar da wani rudani, tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon ne ogan dukkan wani shugaba a kasarnan Saboda shine yayi mulki zango daya tilo mafi tsawo wanda babu tangarda a kasarnan. Ya girmi kowa. Kuma aduk sanda yake da wata shawara me amfani yakan je fadar shugaban kasane ya fada.

Duk da dai Festus be ambaci sunan Obasanjo ba amma ana iya fahimtar wannan rubutu nashi martanine kai tsaye ga maganar Obasanjo.

No comments:

Post a Comment