Saturday, 30 March 2019

'APC za ta fara zawarcin ‘yan PDP'


Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya kuma tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai Farouk Adamu Aliyu ya bayyana cewa jam'iyyarsu ta APC ta koyi darasi dangane da yadda aka gudanar da zabubbukan kasar.

A wata hirarsa da ya yi da BBC ya bayyana cewa dauki dora ko kuma kakaba 'yan takara na daya daga cikin abubuwan da suka kawo ma jam'iyyar tasgaro ya zama cewa ta fuskanci matsaloli a wasu jihohi wanda hakan ya yi sanadiyar rasa wasu kujerun gwamnoni da ma na 'yan majalisa.

Ya bada misali da jihar Ogun inda ya bayyana cewa gwamnan ya yi ungulu da kan zabo inda gwamnan jihar dan APC ne amma ya jagoranci wata jam'iyya domin ganin cewa an kada jam'iyyar APC a zaben gwamna.

Ya kuma ba da misali da jihohin Imo da Bauchi da kuma Adamawa inda ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida ne suka yi sanadiyar faduwar jam'iyyar zabe a jihohin.

Ya yi kira ga jam'iyyar APC mai mulki a kasar kan cewa a shekarar 2023 ta tabbatar an yi zaben fitar da gwani na jam'iyyar sahihi kuma ingantacce a duk fadin kasar.

Farouk Adamu ya kuma yi hannunka mai sanda ga Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari inda ya ce ''shugaban ya ga yadda jama'ar kasar suka nuna masa soyayya a duk jam'iyyar da ya shiga har ya zama shugaban kasa don haka akwai hakkin mutane a kansa na ya tabbatar da cewa jam'iyyar APC ta dore.''

Tun bayan nasarar da jam'iyyar APC ta samu a zaben 2015 ta ke fama da rikice-rikicen cikin gida wanda hakan ya yi sanadiyar da dama daga cikin jiga-jigan 'yan jam'iyyar suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Sai dai Farouk Adamu ya kara bayyana cewa za su ci gaba da zawarcin wadanda suka sauya sheka suka bar jam'iyyar APC domin ganin cewa an jawo su domin tafiya tare.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment