Friday, 29 March 2019

Ba lallai Ronaldo ya buga wasan Juventus da Ajax ba

A yayin da kungiyar Juventus ke tunkarar wasan da zata buga da Ajax na gasar cin kofin zakarun turai a watan gobe, tauraron dan wasanta, Cristiano Ronaldo ya samu rauni a wasa na farko daya bugawa kasarshi tun gasar cin kofin Duniya. Duk da Ronaldon yace ciwon da yaji ba wani me tsanani bane sosai, nan da sati daya ko biyu zai dawo, Juve tace ba lallai ya dawo nan kusa ba.Da yake magana da manema labarai, shugaban Juventus din, Andrea Agnelli ya bayyana cewa, idan mutum ya ji irin ciwon, da Ronaldo yaji, ya kamata abi a hankali.

Yace Ronaldon yana nan Qalau kuma zasu bashi kariya har zuwa karshen kakar wasan domin hakan yafi muhimmanci fiye da wasa daya.

No comments:

Post a Comment